Dalilin da yasa aka saki murja kunya
Dalilin da Ya Sa Aka Fitar da Murja Kunya Daga Gidan Gyaran Hali, Gwamnatin Kano Ta Magantu Litinin, Faburairu 19, 2024 at 6:25 Yamma daga Sani Hamza Gwamnatin Kano ta ce ba za ta tsoma baki a shari'ar da ake yi da shahararriyar 'yar TikTok, Murja Ibrahim Kunya ba. A cikin wata sanarwa ta hannun kwamishinan watsa labarai na jihar, gwamnantin ta kuma ce ba ta da hannu a sakin Murja daga gidan yari Idan ba a manta ba, an kama Murja tare da kulle ta a gidan gyaran hali biyo bayan tuhumarta da ake yi da laifin yada bidiyon baɗala a TikTok Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi! Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida. Jihar Kano - Gwamnatin jihar Kano ta ce ba za ta tsoma baki a shari'ar da ake yi da shahararriyar 'yar TikTok Murja Ibrahim Kunya ba. Hakazalika, gwamnatin ta ƙaryata jita-jitar da ake yadawa na cewar tana da hannu a cire Murja daga gidan yari a karshen makon da ya gabata.
Comments
Post a Comment